Me ka ke nema?


Shafin Farko

Kasuwar Ujile



Goro


Gabatarwa

Kasuwar Ujile, kasuwa ce ta ƙasa-da-ƙasa wacce take a garinKanowacce take aƘofar Mazugal. Tana Arewa da Ƙofa daga waje, sannan kumaGanuwar Kanotana bayanta daga Yamma. Gabanta kuma titinIbrahim Badamasi Babangidane daga Gabas. Damanta kuwa, mararrabar titin da ya fito daga ƙofa ne daga Kudu kenan. Sai kuma Arewa da ita; daga hagu kenan, tana iyaka da Filin Dalar Gyaɗa.

An kafa wannan kasuwa a tsakankanin shekarar 1953 zuwa 1960 a zamanin mulkin Sarkin KanoMuhammadu Sanusi I (1953 – 1963).

Da farkon farawa, shekaru aru-aru da suka wuce, fatake kan tafi Yankin Gwanja wadda a yau yake cikin ƙasar Ghana su sayo goro su kawoKasuwar Kurmida ke cikin birnin Kano. Wasu kuma da suke a wajen Kano sukan ajiye hajojinsu a gidaddajinsu masaya su je su saya su kai kasuwannin da suke da buƙata su sayar.

Sannu a hankali har aka gano kurmin goron da ke jahar Abekuta aNajeriyadaga baya kuma jahar Ondo. Aka sake samun ƙarin wata dama ta cinikayyar goro. Mutanen da ke harkar wannan yanki na Abekuta sukan tafi ne a kanjakunakamar yadda Alhaji Adamu Abubakar ya gaya mana a cikin tattaunawar da muka yi da shi. Wata magana da ya furta mana wacce zan so masu karatu su sani domin hikimar da ke tattare da basira irin tadabbob, ita cewa, ya ce: “Ni tushenmu daga garin Gulu ne wacce a yanzu take cikin ƙaramar hukumar Rimin Gado ajahar Kano. Kuma mahaifana sana’arsu kenan fataucin goro. To idan goronmu ya ƙare a lokacin ina ƙaramin yaron da bai haura shekara bakwai zuwa takwas ba, akan ɗoro ni a kan jaki bayan an idar da sallar Isha. Da zarar an ɗoro ni a kan jakin nan sai a ƙulle min kuɗina a cikin rigata waɗanda basu haura sule ɗaya da rabi ba. To wallahi ko ina barci a kan jakin nan zai kamo hanya tiryan-tiryan sai ya zoƘofar Kabugaya tsaya. Saboda a lokacin ana rufe ƙofofin shiga gari da daddare sai da asuba a buɗe. Ni kuma da zarar ya tsaya zan farka na san an zo Ƙofar Kabugana sauka na ɗaure shi. Lokacin akwai rijiya a Ƙofar. Idan Asuba ta yi aka yi sallah, sai sarkin ƙofa ya buɗe ƙofa kowa ya shigo gari ya tafi gurin da zai je. Ni da na shigo gari sai na wuce kai tsaye zuwa Kasuwar Kurmi na sayi kwance kuɗin daga rigata na miƙa. Sai a zuba min fakani (Duk fakani ɗaya daidai yake da ƙwarya ƙwarya ɗaya, ƙwarya ɗaya kuma ƙwayar goro ɗari kenan)  ashirin na goro a mangala ta. Kowane gefe goma-goma. Sai na hau tsakiya na zauna, sai gida”.


Goro

Lokacin da Bature ya zo, sai ya zo da fasahar jirgin ƙasa. Saboda haka sai fataken da ke zuwa wancan yankin Gwanjar Abekuta suka koma suna ɗoro goronsu daga can a taragun jirgi. Idan suka sauke a tashar jirgi, sai masaya su bisu har can su saya. To haka abin yake ga sauran kayayyaki ma da fatake suke ɗoro wa a jirgi.

Da abubuwa suka fara bunƙasa, sai masu jirgi suka ce kowa ya fice ya basu guri. Saboda haka sai iyayenmu suka tafi gurin sarki; a lokacin Mai Martaba Sarkin Kano Muhammadu Sanusi I ne yake sarauta (Kakan sarki mai ci yanzu kenan, Muhammadu Sanusi II), suka kai kokensu. Da sarki ya ji abin da ke tafe da su, sai ya ce: “To, ku tafi Ƙofar Mazugal akwai fili yana nan na gwamnati, wanda Alhassan Ɗantata ya ɗiba ya bar saura. Idan ya yi muku ku dawo ku gaya min”.

Da jama’a suka je suka ga fili ya yi musu, sai suka koma suka sanar da sarki. Sai sarki ya ce da su: “Za a je a karkasa muku kowa a bashi. A ware na gwamnati daban, a ware na ‘yan kasuwa daban.” Daga nan sarki ya sa aka gina dogwayen rumfuna “Su ne dogwayen sito-siton can da ka ke gani”, ya ce da ‘yan kasuwa: “Duk wanda ya kasa kayansa bai sayar ba, to ya ɗauke ya kai cikin waɗancan rumfuna ya adana. Sai gobe ya fito da kayansa ya sake kasawa”. Sannan kuma ya ce duk wata ga abin da za a riƙa bayarwa har mutum ya mallaka. Wannan shi ne yadda aka kafa wannan kasuwa.

Bayan an kafa kasuwar kuma, sai aka yi titin jirgi daga tasha zuwa kasuwar sannan ya zarce Filin Dalar Gyaɗa. Idan ya zo ya sauke goro, sai kuma ya ɗebi gyaɗa da shanu daigiyar kabada ake ɗaure huhun goro da ita ya tafi da su.


Huhun Goro

Saboda haka aka gina waccar karar shanu (Wacce daga baya aka gina mayanka a kusa da ita), duk a lokacin sarki Muhammadu Sanusi I aka gina su. Sai dai ita karar bata bunƙasa sosai ba. An yi wani guri da ake ajiye taragun jirgi a bakin ƙofa, sai kawai a koro shanu su shiga ciki. Sannu a hankali wannan kasuwa ta tashi ta koma Mariri.

Kayayyaki

Babu wata haja da ake kasawa a wannan kasuwa da ta wuce goro. Ana iya samun na’ukan goro da suka haɗa da Goriya (Goro mafi girma), Sara (Shi yake biye wa Goriya a girma), Farsa (Ɓarin goriya da yake rabe wa biyu da kansa), Ninu (Mafi ƙanƙatar goro) da kuma tsinta (Goro mai tsutsa kenan da ake cire wa daga cikin mai kyau).


Farsar Goro

Abokan Hulɗa

Ana hulɗa da kusan garuruwa da dama a ciki da wajen Najeriya a wannan kasuwa. Abin da ya shafi ƙasashen waje daga wannan kasuwa ana kai kaya zuwa ƙasashen da suka haɗa da Bahrain, Yemen, Saudi Arabia, Sudan, Nijar, da Chadi. Wasu kai tsaye, wasu kuma daga wasu ƙasashen ake wucewa da shi.

Wannan kasuwa tana da sauƙin zuwa. Kasantuwar ta samu kyakkyawan matsugunni. Bata da nisa da filin jirgin saman Malam Aminu Kano wanda yake na ƙasa-da-ƙasa ne. Sannan kuma bata da nisa da Tashar Mota ta Ƙofar Ruwa. Haka nan kuma bata da nisa da babbar Kasuwar Sabon Gari da ke Kano. Kuma dai tana kusa da katafariyar Kasuwar Ƙofar Wambai.

Manazarta:


Tattaunawa da Alhaji Adamu Abubakar wanda aka fi sani da Ɗan’azumi a Kasuwar Ujile a ranar 30/12/2018.


Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub